A karo na biyu an gurafanar da sanannen mai sacewa da garkuwa da mutanen nan na jihar Legas da aka fi sani da suna Mr Evans, a gaban wata babbar kotu a jihar.
Jami’an ‘yan sanda sun gurafanar da Evans, gaban wani alkali, Mr Oluwa Toyin Tayo, inda aka gudanar da kwaskwarima a kan cajin da ake masa da yanzu ya hada da sace mutane da kisan kai da kuma mallakar makamai ba tare da izini ba, wannan caji ya banbanta da na farko da aka yi masa inda aka gurafanr da shi gaban wani alkali justice Hakim Oshodi.
Yanzu haka dai alkalin kotun ya tsayar da ranar juma’a mai zuwa a matsayin ranar da za a cigaba da sauraren wadannan sababbin cajin da aka gurfanar da Evans a kai.
Barista Alhaji Danlami Wushishi, masanin harkokin shari’a ne, ya bayyana cewa a duk lokacin da aka sami shaida akan zargin Evans, da aikata wani laifi, cajin da ake masa na iya sauyawa, dan haka wannan ba lallai ya kawo tsaiko ga tuhumar da ake masa ba.
A daya bangaren kuma, Justice Muhammed Idris, na babbar kotun tarayya dake Legas, ya umurci rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta biya surukin Mr Evans, mr Mr Okechukwu Obichina, wanda take ci gaba da tsarewa duk da umurnin da aka bada na cewa a sake shi kudi Naira Miliyan Biyu.
Domin karin bayani, saurari rahoton da Babangida Jibrin ya aiko mana.
Your browser doesn’t support HTML5