Hukuncin da kotun ta bayar, ya biyo matakin dake tabbatar da hukuncin kotun farko, cewa ba ta same su da aikata laifi kowane iri ba. A lokacin zaman kotun, alkali ya sallame su daga gidajen Yarin da suka shafe watanni hudu saboda zargin sun gudanar da zanga zanga ba da izinin hukuma ba.
Nouhou Arzika, da Ali Idrissa, da Moussa Tchangari, da kuma Lirwana Abdourahama ne suka daukaka kara, saboda a cewarsu ba su gamsu da hukuncin watanni uku da kotun ta ce shi ne hukunci dake dai dai da abin da suka aikata ba.
Bayan shafe watanni sama da 12 akan wannan magana, kotun daukaka kara ta birnin Yamai ta wanke wadanan 'yan fafuta na gamayyar kungiyoyin CCAC masu kin jinin dokar harajin 2018.
Kotun ta umurci hukumomi su biya wadanan mutane diyya daga asusun baitilmalin kasa, koda yake ba ta kayyace adadin kudaden da ya kamata a biya ba, sai dai Nouhou Arzika na MPCR na cewa ba haka suka so ba.
Har yanzu lauyan gwamnati bai bayyana matsayinsa akan hukuncin kotun daukaka kara ba, yayin da kungiyoyin gamayyar CCAC suka lashi takobin ci gaba da gwagwarmaya don ganin an sallami sauran da ake tsare da su a gidan Yari.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5