Wata kotu a Amurka ta samu shahararren mawakin zamani R. Kelly da laifin yin mu’amulla da ta shafi yin badala da mata da kananan yara.
Samun R. Kelly da wannan laifi na zuwa ne bayan da mawakin da ya shahara da wakarsa ta “I Believe I Can Fly” ya kwashe gomman shekaru yana kaucewa fushin hukuma kan zarge-zargen da ake ta yi akansa, kan yadda yake ajiye kananan yara a gidansu don yin ayyukan masha’a da su.
Wani gungun masu taimakawa alkali wajen yanke shari’a mai dauke da maza bakwai da mata biyar ne suka samu R.Kelly da laifukan da ake zargin shi da su.
Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa, yayin da ake karanto laifukan da ake tuhumar mawakin akan su, an gan shi ya sunkuyar da kai a kotun.
Tuhume-tuhumen da aka yi wa mawakin mai shekara sun dogara ne akan shaida da manajojinsa da hadimansa suka bayar kan yadda suka taimaka masa wajen cimma wannan buri nasa na ajiye ‘yan mata tare da hana su yin magana – wanda laifi ne babba.
Wadanda suka zargi R. Kelly da laifukan, sun ba da shaida a lokacin shari’ar, inda suka ba da bahasin cewa Kelly ya ci zarafinsu a lokacin suna ‘yan matasa.
Lauyan Kelly Deveraux Cannick ya ce nuna takaicinsa kan yadda masu taimakawa alkalin suka yanke wannan hukunci.