Kotu Ta Sallami Bello Bodejo Bayan Antoni Janar Ya Janye Tuhumar Da Ake Masa

Kungiyar Fulani makiyaya ta MIYETTI ALLAH KAUTAL HORE

A hukuncin daya zartar, Mai Shari'a Ekwo ya sallami Bodejo ne bayan da lauyar dake kare ofishin antoni janar din, Aderonke Imana, ta gabatar da bukatar tare d neman janye tuhume-tuhume 3 da suka gabatar.

Mai Shari'a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ya wanke shugaban kungiyar fulani makiyaya ta "Miyetti Allah Kautal Hore", Bello Bodejo, daga zargin aikata ta'addanci da Ofishin Babban Lauyan gwamnati kuma Antoni Janar na tarayya ke yi masa.

A hukuncin da ya zartar, Mai Shari'a Ekwo ya sallami Bodejo ne bayan da lauyar dake kare ofishin antoni janar din, Aderonke Imana, ta gabatar da bukatar tare da neman janye tuhume-tuhume 3 da suka gabatar.

A cewar lauyar, bukatar tana karkashin sashe na 108 na dokar hukunta manyan laifuffuka ta 2015.

Lauyan dake kare Bodejo bai kalubalanci bukatar ba, inda ya godewa ofishin antoni janar din.

Daga bisani, jagoran lauyoyin dake kare Bodejo, Ahmad Raji, ya nemi kotun da ta sallami wanda ake zargin karkashin sashe da bangaren da masu kara ya gabatar.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu Ta Saki Bello Bodejo. mp3