Kotu Ta Sa A Tsare Alhassan Ado Doguwa A Gidan Yari

Alhassan Ado Doguwa lokacin da jami'an hukumar gyara hali za su kai shi gidan gyara hali

A zaman farko na ranar Laraba, alkalin kotun ya dage sauraren karar zuwa ranar 7 ga wannan watan nan na Maris.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya ta gurfanar da shugaban majalisar wakilan kasar Alhassan Ado Doguwa a gaban kotun majistire ta jihar.

Ana tuhumar Doguwa da hannu a tarzomar zabe, inda wasu mutane uku suka rasa rayukansu a yankin mazabarsa.

Alkalin kotun mai shari’a Ibrahim Mansur Yola ya ba da umurnin tsare Alhassan Ado a gidan kurkuku ko cibiyar gyaran hali ta Goron Dutse da ke birnin Kano.

Daga bisani, alkalin ya dage saurarn karar zuwa ranar 7 ga wannan wata na Maris lokacin da kawo batun neman a ba da shi beli.

A shekaranjiya litinin ne tarzoma ta barke a garin Tudunwada tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da NNPP, al’amarin da yayi sanadiyyar mutane akalla uku yayin da wasu da dama suka jikkata.