Kotu Ta Kwace Dala Milyan 4 Da Dubu 700 Da Naira Milyan 830 Da Sauran Kadarori Daga Hannun Emefiele

Tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele

Mai Shari'a Yellim Bagoro ne ya bada umarnin a jiya Alhamis 23 ga watan Mayun da muke ciki, sakamakon bukatar da lauyan Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, Bilkisu Buhari, ta gabatar.

Babbar Kotun Tarayya dake Legas ta bada umarnin wucin gadi na kwace fiye da dala milyan 4 da dubu 700 da naira miliyan 830, da sauran kadarori da dama dake da alaka da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mr. Godwin Emefiele.

Mai Shari'a Yellim Bagoro ne ya bada umarnin a jiya Alhamis 23 ga watan Mayun da muke ciki, sakamakon bukatar da lauyan Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, Bilkisu Buhari, ta gabatar.

Bayan sauraron lauyan Hukumar EFCC, a hukuncin data zartar, Mai Shari'a Yellim Bagoro tace, "na saurari hujjojin lauyan masu kara sa'annan na nazarci bukatar da aka gabatar tare da takardun dake mara mata baya.

An bayyana cewar kudaden da za'a mayarwa gwamnatin tarayya a matakin wucin gadin na ajiye ne a bankunan "First da Titan da Zenith wadanda Omoile Anita Joy da kamfanonin "Deep Blue Energy Services Limited da Exactquote Bureau de Change Ltd da Lipam Investment Services Limited da Tatler Services Ltd da Rosajul Global Resources Ltd da kuma Til Communication Nigeria Ltd ke gudanar dasu.

EFCC ta doshi kotu ne domin neman kwace kudaden a matakin wucin gadi, karkashin sashe na 17 na dokar yaki da zambar kudade ta 14 ta 2006, da sashe 44(2)(b) na kundin tsarin mulkin Najeriya kuma karkashin hurumin kotun.