Kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar da nasarar da Gwamna Nasir Idris ya samu a zaben gwamnan jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A ranar Juma’a kotun karkashin Alkalai uku ta ce daukaka karar da jam’iyyar PDP da dan takararta General Aminu Bande suka yi ba ta da tushe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Alkalan kotun karkashin jagorancin Justice Ndukwe Anyannwu, sun ce dukka al’amura guda biyar da aka bijiro da su a shari’ar, Gwamna Idris ne mai gaskiya ba PDP ba.
Justice Anyanwu ta ce zargin gabatar da shaidar kammala karatu da aka gabatar akan mataimakin Gwamna Abubakar Umar Tafida ba ya cikin abin da doka ta ce ya zama wajibi a gabatar.
Hukuncin na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan yadda kotunan daukaka kara a Najeriya ke rushe zabukan gwamnoni galibi na jam'iyyun adawa.