Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage ci gaba da sauraron karar da gwamnati ta shigar da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, kan zargin aikata ta’addanci da cin amanar kasa har sai abin da hali ya yi.
Mai shari’a Binta Nyako ce ta dakatar da shari’ar saboda akwai daukaka kara da gwamnatin tarayya ta yi, kan hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke a ranar 13 ga watan Oktoba.
Hakan na faruwa ne yayin da shi ma Kanu ya ki yarda ya bayyana a gaban kotu saboda yana kulabalantar kin bin umarnin kotun daukaka kara da hukumomi suka yi, bayan da aka wanke shi daga wasu laifuka.
Ko mene ne ake nufi da dakatar da shari’ar Nnamdi Kanu mai taken Sine die, Masanin shari’a barista Haruna Magashi ya ce kotu ba ta yi kuskure ba saboda lamarin abu ne sananne a bisa doka.
Al’amarin na shari’ar Nnamdi Kanu dai ya kawo tsaiko ga wasu kararraki guda biyu da aka gabatar da su a gaban babbar kotun tarayyar kasar inda aka dakatar da su har sai abin da hali ya yi, saboda wannan dalilin na shari’ar da ake yi wa Kanu.
A wani bangare kuma, fitaccen lauya Barrister Mainasara Kogo ya ce idan har aka jinkirta yanke hukunci a kotun kolin kasar hakan na nufin za’a yi zagon kasa ga sashe na 36 na kundin tsarin mulkin kasar da kuma nakasu ne ga doka ta hanzarta shari’o’i da ake da ita a Najeriya.
Duk kokarin jin ta bakin gwamnati a kan lamarin ta wayar tarho da sakon tes ya ci tura.
A yanzu dai ‘yan kasa da masu bibiyar sahri’ar za su zuba ido su ga iya tsawon lokacin da za’a diba kafin adawo kan ta.
Saurari cikakken rahoton Halima AbdulRa'auf:
Your browser doesn’t support HTML5