A ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba ne wata kotun daukaka kara ta tarayya a Abuja, karkashin jagoranci mai shari’a Hannatu Sankey ta yanke hukunci wanke Nnamdi Kanu an kan cajin da aka yi masa bayan kamo shi daga kasar Kenya.
A hirarshi da Muryar Amurka, Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce maganar saki ko maganar shirin saki bata taso ba kamar yadda yake ta fuskar tsarin ma’amalar shari’a. Bisa ga cewarsa, ita wannan shari’a ko kuma wannan hukunci da aka yi kacokan ya dogara ko ya ta’allaka kan ma’amalar da ake da’awar cewa ainihin an kawo shi Najeriya ta karfin tsiya daga Kenya ba’a kan tsari na doka ba.
“Idan ma shi hukunci yana iya tsayawa ko ya inganta to kafin Nnamdi Kanu ya arce ya bar Najeriya akwai caji wanda yake wanzuwa wanda yake ingantacce gaban kotu, idan kana tunawa ya arce ya tsallake beli bayan an gurfanar da shi gaban kotu, kuma wadannan caji babu wani hukunci na kotu a kansu caji ne da ake bin bahasin su a gaban kotu,” in ji Malami.
Ya ce saboda haka idan ana maganar bayan ya arce yaje Kenya kuma akwai abubuwa wadanda suke gaban kotun tana dubawa kafin ya arce zuwa Kenya, saboda haka hukunci a kan daya daga cikin bangare da ke cikin al’ammuran da ke a gaban kotu zai zama wajibi ba zai zama wato yana aiki a kan sauran caje-caje wadanda suka gabaci kafin arcewarsa zuwa Kenya ba.
Ya kara da cewa, "idan kotu ta yi hukunci idan ba kotun koli ba ce, akwai dama ta daukaka kara, akwai damar ta warware hukuncin da kuma damarmaki daban da shari’a ta zo da su, kuma ala kulli hali a cikin wannan yanayi dai matsayin shi ne gwamnati za ta duba matsayin da take da shi ta fuskar shari’a ta kuma yiwa mutane adalci."
Amma kamar idan za’a iya tunawa irin wannan shari’ar banbancinta da matsalar da ta haddasu a Amurka ta fuskar bin-Ladan kalilance idan har ma akwai banbanci, abin da ya faru a Amurka ta dauki matakin da ta dauka a kan bi-Ladan na zuwa wata kasa ma tatabbatar bin-Ladan bai wanzuwa ba shine kisa da ingiza mutane su yi kisa a kan Amurka da 'yan kasa baki daya.
Wannan kuma shine abin da ke wanzuwa ko ya wanzu a cikin wannan yanayi, kuma ala kulli halin matakin da ya kamata gwamnati ta ci gaba da dauka har a kai makura don tabbatar da cewa an yiwa al’umma adalci an kare dukiyoyinsu , rayukansu da hukumominsu.
Da yake amsa tambaya ko akwai alamar takun saka ne ko rashin jituwa tsakanin bangarorin gwamnati ko na zartarwa da na shari’a shi ya sanya ake yin irin wannan bita da kulli, Minsitan shari’a Malami ya ce wannan ba tambaya ce da zai iya amsawa ba kuma ala kulli hali shi ne hakkin gwamnati da ofishin atoni janar shine na tabbatar da cewa an yi kariya game da hakkokin al’ummar kasa ba kariya a kan hakkokin mutum daya ba kuma za su ci gaba da yin aiki ta wannan fuskar.
Saurari cikakken hirar cikin sauti: