An Bada Umarnin Mayar Da Dino Melaye Asibiti

Dino Melaye

Wata babbar kotu a jihar Kogi ta bayar da umarnin a mayar da Sanata Dino Malaye babban asibitin Abuja domin a ci gaba da kula da lafiyarsa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

A cewar jaridar, Lauyan da ke kare Sanata Dino Melaye wato Mike Ozekhome, shine ya nemi Alkali Nasiru Ajanah da ya bada belin wanda yake karewa, wanda kuma yanzu haka yake fama da rashin lafiya.

Alkalin ya ce kotu zata duba bayanan neman belin da aka shigar gabansu zuwa ranar Litinin. Ranar Alhamis 14 ga watan Mayun 2018 din da muke cikin ne wata kotun Majistare ta bada umarnin ci gaba da rike ‘dan Majalisar Dattawan.

Sun kuma yi hukuncin ne bisa rashin gamsuwa da hujjojin neman bada belin da lauyan Melayen ya gabatar. Rundunar ‘yan sandan Najeriya ce ta gurfanar da Dino a gaban kotun, bisa tuhumarsa da tallafawa ‘yan bindiga da kuma mallakar makamai.

‘Yan sandan dai sun kai Sanatan ne zuwa kotu ranga-ranga akan amalanken tura marasa lafiya. Wasu daga cikin al’ummar jihar Kogi dai na kallon lamarin tamkar wani cin zarafi ne ga Dino, ganin yadda zaben kasar na 2019 ke kara kusantowa.

Masanin kundin tsarin mulkin kasa a Najeriya wato Barista Shehu Kagara, yace akwai yakinin cewa, Sanatan ba zai rasa Lauyan da zai wakilce shi a Kotu ba, don haka daukarsa ranga-ranga cikin halin rashin lafiya zuwa kotu, hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.