Kotu Ta Ba Da Belin Kanu Saboda Rashin Lafiya

Nnamdi Kanu yayin da ya bayyana a gaban kotu a Abuja. Jan. 20, 2016

Wata kotun tarayya a Abuja, Najeriya, ta ba da belin daya daga cikin masu jagorar fafutikar samar da kasar Biafra, Nnamdi Kanu, bisa dalilai na rashin lafiya, kamar yadda shafukan yanar gizon jaridun Najeriya da suka hada da Daily Trust da Punch suka wallafa a yau.

Kanu ya kwashe kusan shekaru biyu a tsare a gidan kurkuku ana tuhumar shi kan laifukan da suka da alaka da cin amanar kasa.

Mai shari’a Binta Nyako ta ce ta ba da belin Kanu ne saboda ya na fama da rashin lafiya.

Wannan shi ne karon farko da aka ba da belinsa bayan yunkurin neman hakan a baya ya cutura.

Wasu daga cikin sharuddan da kotun ta gindayawa Kanu a ke kuma so ya amince da su kafin a sake shi sun hada da:

  • Gabatar da mutane uku da ke da miliyan dari-dari
  • Ba a amince ya yi magana da ‘yan jarida ba
  • Ba a yarda ya hada gangami ba
  • Ka da kuma ya shiga taron jama’a da suka haura mutum goma

Baya ga wadannan sharudda, mai shari’ar ta nemi Kanu da ya amince zai rika gabatar da kansa a duk lokacin da aka nemi ya yi hakan a gaban kotun.

A halin da ake ciki, an mayar da Kanu zuwa kurkukun Kuje dake birnin Abuja har sai ya cika sharuddan farko da ake bukata.

An dage zaman kotun sai zuwa ranar 11 da 12 na watan Yulin wannan shekara domin ci gaba da sauraren shari'ar.

Tun a ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 2015 jami’an tsaron Najeriya suka kama Kanu a lokacin da ya isa kasar daga London.