Shugaban kungiyar alkalami ta magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari reshen jihar Adamawa Alhaji Ibrahim Bappa Waziri ya furta hakan a wata ganawa da ya yi tare da takwaransa na kungiyar shinkafa da wake, Husseini Gambo Na Kura da manema labarai a Yola fadar jihar
Sun yi barazanar shiga kafar wando daya da wakilan jiha a Majalisar Dattawa da ta Wakilai kan abinda suka bayyana da hada kai da wasu wakilan majalisun tarayya wajen yi wa kudurori da manufofin gwamnatinBuhari zagon kasa.
Alhaji Ibrahim Bappa Waziri ya yi kira ga wakilan Majalisun su himmantu wajen gaggauta aiki akan kasafin kudi na 2017, kudirin dokar kotu ta musamman don yaki da cin hanci da rashawa ta 2015, ba da kariya ga masu fallasa cin hanci da rashawa da kuma tantance kwamishinonin zabe ashirin da bakwai ba tare da sharadi ba.
Shi ma da yake fayyace matsayin kungiyar shinkafa da wake Husseini Gambo Na-Kura ya yi barazanar yi wa ‘yan majalisar kiranyo idan har ba su canja ba ta hanyar soma gangamin fadakar da talakawa dangane da irin lahani da kuma gurgunta kudurori da manufofin da gwamnatin tarayya ta gabatar gaban majalisun tarayya ke yi wa tattalin arziki da tanadar muhimman kayayyakin jin dadin rayuwa ga talakawa.
Kungiyoyin biyu sun alakanta tafiyar hawainiya da ake samu wajen aiwatar da muhimman ayyukan da talakawa Najeriya zasu anfana garesu da son rai da ‘yan majalisun tarayya ke nunawa wajen gudanar da aikinsu.
Saurari Karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.
Facebook Forum