Kotu Ta Ba Da Belin Emefiele

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele

Wannan shi ne karon farko cikin wata guda da Emefiele ya fito baina jama’a tun bayan da aka dakatar da shi fiye da wata guda.

Wata kotu a Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ba da belin tsohon Gwamnan Babban Bankin kasar Godwin Emefiele da aka dakatar wanda ake zargi da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

A ranar Talata Emefiele ya bayyana a gaban kotun inda ya musanta zargin da ake masa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Rueters ya ruwaito wani gidan talabijin.

Kotun ta ba da belin Emefiele akan Naira miliyan 20.

Wannan shi ne karon farko cikin wata guda da Emefiele ya fito baina jama’a tun bayan da aka dakatar da shi fiye da wata guda.

Sharuddan da kotun ta gindaya gabanin ba da belin sun hada da gabatar da wani da ke da kadara a unguwar Ikoyi da ke Legas da wanda shi ma zai biya miliyan 20, mika fasfo dinsa da kuma gabatar da wani ma’aikacin gwamnati da bai gaza kai wa mukami na 16 ba.

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta tsare Emefiele ne a ranar 10 ga watan Yuni, kwana guda bayan da sabon shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da shi.

A kuma wannan watan ne wani alkali ya umurci hukumar da ta shigar da kara ko kuma ta sake shi.

Emefiele dai ya ki amsa laifuka biyu da ake tuhumar shi akai, wanda suka hada da mallakar makami da alburusai ba bisa ka'ida ba, a cewar gidan talabijin na Channels TV.

Ya kuma kalubalanci yadda ake tsare da shi, kuma ya shigar da karar neman beli.

Lauyoyin gwamnati sun bukaci kotun a watan Yuni da ta ba da izinin tsare Emefiele bisa zargin almubazzaranci na wasu kudade da kuma “laifi na cin amana,” tuhume-tuhumen da idan har aka tabbatar da su za a iya daure shi na tsawon lokaci.

Don haka lauyoyin suka samu umarnin kotu na ci gaba da tsare Emefiele har sai an ci gaba da bincike.

Emefiele ya yi kaurin suna wajen yin amfani da wasu irin tsare-tsare da ba wasu ke ganin ba su dace ba na neman kara karfin darajar Naira, da kuma ba da rance ga ‘yan kasuwa kai-tsaye don kokarin bunkasa ci gaba.

Tinubu, wanda ke gudanar da sauye-sauye gadan-gadan a kasar da tafi sauran kasashen nahiyra Afirka karfin tattalin arziki ya soki manufofin Babban Bankin kasar karkashin Emefiele a bikin rantsar da shi a watan Mayu.

A ranar Talata babban bankin kasar ya bayyana matakin farko na kudin ruwa tun bayan dakatar da Emefiele. Daya daga cikin mataimakan Emefiele, Folashodun Shonubi, shi ne a yanzu a matsayin mukaddashin gwamnan babban bankin na kasar.

-Reuters

Saurari karin bayani daga Babangida Jibril:

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu Ta Ba Da Belin Emefiele.mp3