Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya kalubalanci matakin bai wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya na CBN, Godwin Emefiele dama ya tafi hutun karo karatu.
A makon da ya gabata rahotanni sun yi nuni da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sahalewa Emefiele tafiya hutun karo karatu a kasar waje.
Sai dai cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, gwamna Matawalle, ya nemi Buhari da ya soke hutun domin Emefiele na da tarin batutuwan da ya kamata ya yi bayani akai ga sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ke shirin karbar mulki.
“Ina so na yi kira ga Shugaba Buhari, da kada ya amince da hutun zuwa karo karatu ga duk wani ma’aikaci da yake da muhimmiyar rawa da zai taka wajen ganin sabuwar gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta fara aiki.
“Daya daga cikin wadannan mutane da rahotannin kafafen yada labarai ke cewa sun nemi izinin tafiya hutun karo karatu shi ne, Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele.” Matawalle ya ce cikin sanarwar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A cewar Matawalle, akwai bukatar Emefiele ya tsaya ya yi bayani game da “shirin samar da sabbin kudade mara kan-gado” da ya kirkiro, wanda ya jefa al’umar Najeriya cikin mummunan yanayi.
Gwamnan na Zamfara ya kara da cewa, Shugaba Buhari da mai dakinsa suna da kyakkyawar niyyar ganin an mika mulki salim-alim, “amma akwai wasu jami’ai da ke neman su haifar da rudani wajen tabbatar da aukuwar hakan.”
Matawalla sunan Emefiele kadai ya kama, bai ambaci sauran jami’an ba.
Jihar Zamfara wacce ke arewa maso yammacin Najeriya, na daya daga cikin jihohin da suka maka babban bankin na CBN a kotu wajen kalubalantar shirin sauya kudaden da aka yi.
Jaridar ta Daily Trust ta ruwaito cewa fadar gwamnatin ta Najeriya ta ce ba ta da masaniya kan shirin bai wa Emefiele hutun zuwa karo karatu.