Kotu ce Kawai Zata iya Tabbatar da Wannan Ikirarin ko Akasin Haka

Wasu ‘yan majalisar dattawan Najeriya sunyi zargin kundin littafin da akayi amfani dashi wajen samar da shugabancin majalisar na yanzu wadda ake takkadama akansa cewa na jabu ne, a don haka duk abin da akayi daya shafi zabe da ayyuka karkashin ka’idojin dake kunshe cikin wannan littafin ya sabawa doka.

Sai dai lauyoyi sunce kotu ce kawai zata iya tabbatar da wannan ikirari ko akasin haka.

Sanata Kabiru Marafa, ne daga jihar Zamfara, ya fara bujuro da wannan batu a zauren majalisar, a makon jiya, inda ya bukaci a gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiya.

Da alama dai wannan ikirari na Sanata Marafa, yayi daidai dana takwaransa Sanata Barau Jibrin daga Kano.

Barrister Abdu Bulama Bukarti, Malami a tsangayan nazarin aikin Lauya ta Jami’ar Bayero dake Kano yace “ Ranar farko da aka zo zaman majalisa an fito da sabon kundi akace na 2015 ne, kaga tambaya ta farko shine yaushe aka yi gyaran fuska, yaushe ma aka zabi majalisar, yaushe ma majalisar ta zauna aka rantsar da ita, yaushe ta zabe shugabani, yaushe aka bi ka’idar da shashe na dari da goma ya tanada na yadda za’a gyara kundin da za’a zo har ace anyi gyara.”