Koriya Ta Kudu Ta Kalubalanci Koriya Ta Arewa

Sojoji suna dube-dube a garin Paju dake bakin iyakar Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa. Afrilu 25, 2013.

Koriya ta Kudu ta bada shawarar zantawa da Koriya ta Arewa akan masana’antun hadin gwiwar kasashen guda biyu, kuma tana barazanar mayar da martini mai karfi idan KTA bata amince da wannan shawara ba.
Kakakin ma’aikatar hadin kan kasashen, na KTK Kim Hyung-suk shine ya gabatar da wannan shawara yau alhamis.

Kim bai fadi abinda kasar shi ta KTK zata yi ba idan KTA ta ki daukar wannan shawara kafin karfe 12 rana na Juma’a mai zuwa. Sai dai ma’akatar tayi barazanar daukar matakai masu tsauri idan KTA taki amincewa da wannan shawara.

Ayyuka a cibiyar masana’antun ta Kaesong, wanda ke arewa daga bakin iyakar da ta raba KTK da KTA, sun tsaya cak tun bayan da KTA ta janye ma’akatanta a fusace, kuma ta hana ma’aikata daga KTK zuwa cibiyar a farkon wannan wata.

Misalin ma’aikata ‘yan KTK 180 ne suke zaune a cibiyar kamfanonin suna fata za’a dawo da aiki kwannannan, amma abinci da sauran abubuwan bukata sun fara kare musu.