Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 175 Sun Mutu A Bangladesh


Inda ginin masana'antu ya ruguje kennan a kasar Bangladesh.
Inda ginin masana'antu ya ruguje kennan a kasar Bangladesh.

Adadin mutanen da suka mutu bayan rugujewar wani gini dake dauke da masana’antu kayan sakawa a Bangladesh yayi tsalle zuwa 175, yayin da masu agajin gaggawa suke ci gaba da neman wadanda suka rayu. Misalin mutane 1,000 ne suka ji raunuka bayan abkuwar wannan tashin hankali.

Ma’aikatan da suke makale a baraguzen ginin suyi ta jiran masu aikin ceto zu zo su zaluko su tun jiya Laraba bayan da wani gini a garin Savar, dake wajen birnin Dhaka ya ruguje. Mutanen da suka rayu sunce wannan al-amari ya faru ne a cikin dakika kadan.

Iyalai sun taru a wata makaranta dake kusa da inda abun ya faru, kuma inda ake kai gawarwaki domin neman ‘yan uwansu.

‘Yan sanda sunce shugabannin kamfanin sun yi kafar ungulu da kashedin da akayi musu, na cewa kar su bari ma’aikata su shiga wannan gini bayan da aka gano tsagu a jikinsa ranar Talata.

Jami’ai sun ce sun shigar da kara akan wanda ya mallaki ginin, kuma ana tsammani zasu shigar da kara akan shuwagabannin masana’antun.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG