Majalisar Tsaro ta MDD ta Aiyana zama a yau Laraba domin zabe kan takunkumin da zata sakawa Koriya ta Arewa sakamakon yanke tallafin ta na Makamin Nukiliya da kuma shirin Makamai masu linzami.
WASHINGTON, DC —
Ana kyautata zaton jawabin a yayin zaman daga Sakataren MDD Ban Ki-Moon wanda bai cika zuwa zaman zaben wannan majalisa ba.
Zaman Majisar tsaron na baya dai ya bukaci Koriya ta Arewa da ta Bar shirye shiryen ta na Makaman Nukiliya da takeyi sannan kada ta gudanar da gwajin makamin Nukiliya ko kuma makamai masu linzami. Amma Koriya ta Arewa ta take wannan dokoki na duniya a shekaru goma da suka wuce ciki har da gwajin makamin Nukiliya a watan Satumba.
Sabon Takunkumin zai hada da katse fitar da Ma’adanin Kwal da Koriya ta Arewa ke yi, wanda wani jami’in Amurka yace hakan zai katse wannna babbn kaso na samun kudin shiga da haraji ga Koriya ta Arewa da kusa kaso 60 cikin dari wanda yayi daidai da Dalar Amurka Miliyan $700 a shekara.