Yana wannan kiran ne kuwa duk da cewa kotun kolin Amurka ta yanke hukuncin cewa kona tuta wani nau’i ne na bayyana ra’ayin dan kasa, wanda kuma Kundin Tsarin mulki ya bashi wannan hurumin.
A wani sako da ya dora a kan shafinsa na Twitter, Trump yace bai kamata a baiwa kowa daman kona tutar Amurka ba, idan kuwa suka aikata hakan kamata ya yi a hukunta su, watakila ma a kwace ‘yancinsu na zama ‘yan kasa ko kuma a jefasu gidan yari har na tsawon akalla shekara daya.
Sai dai ba a yi gaggawan gano dalilin wannan sako da shugaban mai jiran gado ya dora a kan shafinsa na Twitter ba.
Sai dai sakon nashi ya zo ne yan kwanaki bayan wani mataki da wata jami’a a jihar Massachusetts ta dauka na sauke tutocin Amurka bayan an tuhumi wasu dalibai da kona tutar Amurka saboda fusatar da suka yi na ganin an zabio shi dan takarar na Republican, Trump maimakon Hillary Clinton ta Democrats.
A shekaranjiya Lahadi wasu tsofaffin sojin kasar da gungun wasu masu zanga-zanga suka shirya gangamin nuna adawa da kudurin Jami’ar na kin barin tutar Amurka ta tashi a makarantar Hampshire College dake can Massachusetts.