Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Tace Wanda Ya Kai Hari Jami'ar Ohio Mayakinta Ne


Abdul Razak Artan, wanda ya kai hari jami'ar Ohio da yanzu ISIS tace mayakinta ne
Abdul Razak Artan, wanda ya kai hari jami'ar Ohio da yanzu ISIS tace mayakinta ne

Kungiyar ISIS tace Abdul Razak Ali Artan, wani matashi dan asalin kasar Somalia da yan sanda suka ce ya kai hari da mota da wuka a jami’ar jihar Ohio a ranar Litini, sojan kungiyarsu ne, wanda ya amsa kirar auna mutanen kasashen duniya dake da hannu a rundunar sojojin hadin guiwa da ake fafatawa dasua wasu kasashen ketare.

An bada wannan jawabine a kan dandalin Amaqna yada labaran kungiyar yan bindigan. ISIS ta taba anfani dairin wannan ikirarin a wasu hare-haren da ta kai a can baya. Sai dai babu wani martanin gaggawa daga hukumomin Amurka a kan wannan ikirari na ISIS

Artan ya saka wasu saknoni a kan shafinsa na Facebook mintocikafin harin na ranar Litinin din shekaranjiya, inda ya zargi Amurka da laifinkashe musulmi a kasashen waje kuma ya jinjinawa shehun malamin nan na al-Qaida Anwar al-Awlaki a matsayin jarumi, kamar yanda yan sandan Amurka ke fadawa kafofin yada labarai.

Har izuwa yau dai hukumomi na kokarin gano dalilin da yasa Artan ya kai wannan harin a jami’ar dake birnin Columbus, amma kuma a bayanin da ya rubuta cikin Facebook yace yana son ya hallaka milyoyin abinda ya kira “kafirai” don ja wa Amurka burki daga “tsoma bakin” da take yi a harkokin wasu kasashe.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG