Koriya ta Arewa ta ce har yanzu ana ci gaba da samun ta-da jijiyar wuya tsakaninta da Amurka, kuma an samu ci gaba dan kadan ne ta fuskar diflomasiyya, shekara guda bayan taron koli da kasashen biyu masu takaddama da juna suka yi wanda ya kafa tarihi.
A cewar Jakadan Koriya ta Arewa a Majalisar Dinkin Duniya, Kim Song, wanda ya yi jawabi a ranar muhawarar karshe a babban Taron Majalisar na shekara-shekara, dangantaka tsakanin koriya ta arewa da Amurka ba ta samu ci gaba ba, sannan zaman dardar da ake samu a yankin ruwan Koriya yana nan yadda yake.
Kim ya kuma dora laifin hakan akan “siyasa da takalar fada” da Amurkan ke yi a matsayin abin da ke kawo cikas ga zaman tattaunawan bangarorin biyu, sannan ya yi kira ga hukumomin Washington da su lalubo wata sabuwar hanyar neman maslaha.