WASHINGTON D.C. —
Daya daga cikin jagororin masu zanga zanga a Hong Kong, ya bayyana aniyarsa ta shiga fagen siyasa a yankin domin yin takara.
A jiya Asabar, Joshua Wong ya ce zai yi takarar kujerar gunduma a yankin a zaben watan Nuwamba mai zuwa.
Ya kuma kara da cewa, “lokaci ya yi da za a fadawa shugaban China Xi Jingping cewa, wannan fafutukar ta su ce, wacce za su tunkara komai dacinta."
An dai kwashe watanni ana zanga zanga a yankin na Hong Kong, wacce ake yawan yi a kowanne karshen mako, inda akan yi arangama tsakanin ‘yan sanda da masu boren adawa da shisshigin da China ke yi a yankin.