Koriya Ta Arewa ta sake kama wani dan Amurka, wanda furfesa ne a fannin tattalin arziki, dan shekaru hamsin da wani abu, wanda ya je kasar don koyarwa da kuma tattaunawa kan ayyukan jinkai.
WASHINGTON D.C. - —
Kafar labarai ta Koriya Ta Kudu Yonhap ta ce an kama Tony Kim, wanda kuma ake kiransa da sunansa na Koriyanci Kim Sang-duk, a ranar Jumma'a a Filin Jirgin Saman Kasa da Kasa na Pyongyang.
Kim ya koyar da akantanci a jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Pyongyang na tsawon wata guda, a cewar Shugaban Jami'ar, Park Chan-mo. Kim ya kuma koyar a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Yanbian da ke kasar China kafin ya koyar a Koriya Ta Arewar.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce kare dan Amurka na daya daga cikin muhimman ayyukanta. To amma Amurka ba ta da huldar diflomasiyya da Koriya Ta Arewa, don haka ta na tuntubar Ofishin Jakadancin kasar Swedin da ke birnin Pyongyang ne wajen kokarin kubutar da Amurkawan da aka kama.