Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Na Shirye Shiryen Gwajin Makamin Nukiliya


Amurka tayi imanin cewa China zata yi amfani da kafin fada aji akan Koriya ta arewa

Mataimakin shugaban Amirka Mike Pence yace Amirka tayi imanin China zata yi amfani da tasirinta wajen shawo kan kasar Korea ta arewa tayi watsi da shirin nukiliyar ta.

Yau Asabar Mr Pence yayi wannan furuci a Sydney babban birnin kasar Australia wajen wani taron 'yan jarida na hadin gwiwa da Prime Ministan kasar Malcom Turnbull.

Dukkansu Amirka da Australia suna matsawa kasar China lambar tayi amfani da tasirinta domin Korea ta arewa tayi watsi da shirin nukiliyarta.

A wani labarin kuma cibiyar hadin gwiwa tsakanin Amirka da kasar Korea ta kudu a jam’iar Johns Hopkins nan Amirka ta bada rahoton cewa hotunan tauraron dan Adam da aka dauka na inda Korea ta arewa take gudanar gwaje gwajen makaman nukiliya sun nuna wasu hidimomi dake nuni da cewa ana shirye shiryen yin gwajin makamin nukiliya.

Wannan bayani da aka sa a wani dandalin yanar gizo yace hotunan wurin gwaje gwajen makaman nukiliya ya nuna ana yin wani abu a kusa da wurin

Tun dai shekara ta dubu biyu da shidda kasar Korea ta arewa ta gudanar da gwaje gwajen makaman nukiliya guda shidda cikin harda guda biyu data gudanar a bara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG