An fara gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Faransa, zaben da kasashen duniya suke nazari sosai, wanda rabon da aga irin haka tun shekaru da dama da suka shige.
An dauki tsauraran matakan tsaro sosai bayan harin ta’adanci da aka kai birnin Paris kwanaki kafin ayi zaben da yar takara shugaba Marine Le Pen wadda bata kaunar addinin Musulunci ke kan gaba wajen farin jinni.
An girka yan sanda dubu hamsin da sojoji dubu bakwai ciki harda jami’an tsaro na musamman a titunan kasar a zaman wani bangare na matakan tsaron da aka dauka, a yayinda ake zaman zulumi biyo bayan harin da kungiyar Isis tayi ikirarin kaiwa.
Harin da aka kai tsakiyar birnin Paris ya kashe jami’in yan sanda guda daya da raunana wasu mutane da dama.
Wannan ne zaben farko da za’a gudanar karkashin dokar ta bacin da aka kafa a kasar bayan hare haren da aka kai birnin Paris a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar. Masu lura da harkokin siyasar kasar sun ce, harin da aka kai kasar a makon jiya zai sa wadanda suka cancanci zabe wadanda tunda farko basu niyar fitowa su kada kuri’a ba su fito domin yin zaben.
Facebook Forum