Jaridar tace ta bakin wasu jami’ai da basu yarda a ambaci sunayen su ba, sun ce akwai yiyuwar Korea ta Arewa tana kera akalla makami mai linzami guda watakila kuma biyu a wani wurin binciken ta dake Sanumdong.
Jaridar ta ce wani sabon shaidar yin hakan ko ya hada da hotunan da tauraruwar dan adam ta dauka, wanda ya nuna cewa makamin mai irin wanda yake amfani da mai ne, kuma yana iya kai wa Amurka.
Ko a cikin makon da ya gabata sai da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya ce har yanzu Korea ta Arewa tana samar da man da ake anfani da shi wajen sarrafa makaman kare dangi, duk alkawari da ta yi cewa za ta wargaza makaman nukiliya da ta ke da shi.