Jam’iyya mai mulki a kasar Cambodia ta bayyana cewa, ta lashe dukan kujerun majalusar kasar, abinda ya maida kasar karkashin jam'iyya daya.
A zaben da kungiyoyin fafutuka suka aibata domin dakatar da babbar jam'iyyar adawa, jam'iyyar Cambodians Peoples party tace yanzu ita ke da gaba daya kujerun majalisar kasar 125.
A wata kididdiga da jam'iyyar ta CPP tayi, an gano cewa, mafi yawancin masu zabe sun fi sha'awar kauracewa zaben duk da barazanar da gwamnati tayi akan duk wanda yayi hakan.
A lokacin da aka tambayi kakakin jam'iyyar ko sakamakon zai nuna rashin gaskiya a cikin zaben? Ya bayyana cewa jam'iyyar sam bata damu da suka ba.
Firayim Ministan Cambodia Hun Sen na gab da dorawa a kan shekaru 33 da yayi yana mulki da karin wani wa'adin mulki na shekaru 5, ba tare da hamayya ba. Duk da kuwa kananan jam'iyyu 19 ne suka fafata a zaben, basu samu wani kaso na kirki ba.
Facebook Forum