Masu lura da al'amura na yau da kullum na cewa ga dukkan alamu, har yanzu Korea ta arewa ba ta janye da barazanar da ta ke yi na harba makamai masu linazmi ba, inda a baya-bayan nan ta harba wani da sanyin safiyar yau Talata duk da takunkumin da ake kakaba mata.
WASHINGTON D.C. —
Da sanyin safiyar yau ne Korea ta Arewa ta cilla wani makami mai linzami wanda har ya gitta ta sararin samaniyar kasar Japan.
Wannan gwaji na baya-bayan nan, ya haifar da damuwa tsakanin Japan da kasar Korea ta kudu.
Minti 10 da harba wannan makami a sararin samaniyar kasar Japan ya tarwatse gida uku ya fada cikin Tekun Pacific da ke gabas maso arewacin tsibirin Hokkaido na kasar ta Japan, kamar yadda gwamnatin kasar ta fada.
Sai dai harba wannan makamin bai zame ko wacce irin barazana ba ga kasashen arewacin Amurka kamar yadda Sojojin Amurka suka fada.