Jakadan India a Canada ya musanta cewa yana da hannu a kisan wani shugaban Sikh na Canada da aka kashe a British Columbia a bara duk da cewa gwamnatin Canada ta bayyana sunansa a matsayin wanda ake zargi da kisan gillar.
Sanjay Kumar Verma, wanda aka kora a ranar Litinin da ta wuce tare da wasu jami’an diflomasiyyar India biyar, ya fada a cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na CTV a ranar Lahadi cewa zargin yana da alaka da bita da kullin siyasa.
“Babu komai,” in ji Verma lokacin da aka tambaye shi ko yana da wata rawa da ya taka a harbin Hardeep Singh Nijjar, wanda aka kashe a wajen wata cibiyar al’adu a Surrey, British Columbia a ranar 18 ga watan Yunin 2023.
“Babu wata shaida da aka gabatar. Bita da kullin siyasa ne kawai.”
An tuhumi wasu ‘yan kasar India hudu da ke zaune a kasar Canada da laifin kisan Nijjar kuma suna zaman jiran shari’a.
Firai Ministan Justine Trudeau da ‘yan sandan Royal Canadian Mounted sun fito fili a wannan makon tare da zargin cewa jami’an diflomasiyyar India suna kai hari ga ‘yan awaren Sikh a Canada ta hanyar musayar bayanai game da su tare da gwamnatin su ta gida.