Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wata coci a yankin arewa ta tsakiyar Najeriya a lokacin da suke ibada, inda suka kashe wata mata da karamar ‘yarta, kamar yadda wani jami’in gwamnatin kasar ya bayyana a jiya Litinin yayin da ake farautar wadanda ake zargin.
washington dc —
Maharan da ke kan babur sun isa cocin Celestial ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka harbe mutanen biyu da suka mutu, a cewar Jerry Omodara, babban jami’in tsaro na jihar Kogi.
Cocin tana yankin Lokoja na jihar Kogi mai tazarar kilomita 105 daga Abuja babban birnin Najeriya
Lamarin na ranar Lahadi ya sake sabunta damuwa game da tsaro a gidajen ibada a Najeriya, inda a kalla hare-hare bakwai aka kai kan majami'u ko masallatai a bana.
A cikin watan Yuni, wani kisan kiyashi da aka yi a jihar Ondo ya yi sanadin mutuwar masu ibada 40.
Hukumomin kasar dai na zargin cewa maharan da suka kai harin na baya-bayan nan a Kogi, sun kai hari musamman kan cocin ne da mabiyanta.