Ko Me Ke Sa A Ayyana Zabe A Matsayin Wanda Bai Kammala Ba?

Zaben 2023

Yayin da hukumar zabe ta Najeriya INEC ke shirin gudanar da zabukan cike gurbi na ‘yan majalisar wakilai da na dattawa a wasu jihohin kasar, wasu masu zabe sun nuna damuwa kan matsalolin da suka yi sanadin ayyana zabukan a zaman wadanda basu kammala ba.

Kimanin jihohi 17 ne lamarin ya shafa, ciki har da jihar Sokoto, inda za a gudanar da zaben ‘yan majalisun wakilai da na dattawa a dukan mazabu.

Mazabun ‘yan majalisar wakilai goma sha daya da na dattawa uku da ke Sokoto ne aka ayyana zabukansu a matsayin wadanda basu kammala ba, abinda ake kira Inconclusive.

Ga alama wannan lamari bai yi wa hukumar zabe ta kasa dadi ba, abinda ya sa ta dauki matakin dakatar da kwamishinan zabe a jihar Sokoto, da kuma turo kwamishinan zabe na kasa Manjo Janar M A Alkali ya taimaka wa kwamishinar zabe ta riko don yin gyara a zabukan da ke gaba.

Zaben 2023

A jihar Kebbi da ke makwabtaka da jihar Sokoto, akwai mazabun ‘yan majalisar wakilai biyu na Koko Besse/Maiyama da Arewa/Dandi, da mazabar sanatan Kebbi ta Arewa da aka ayyana zabensu a matsayin wanda bai kammala ba.

Haka kuma, wani bayani da hukumar zaben ta fitar ya nuna akwai jihohi da suka hada da Akwa Ibom, Edo, Imo, Kano, Rivers da Zamfara da ke da mazabun majalisar wakilai biyu a kowacensu, da wasu jihohi bakwai da ke da mazaba daya a kowacensu da zabensu bai kammala ba.

Masana kimiyar siyasa irinsu Farfesa Tanko Yahaya Baba, na Jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto, na ganin akwai abubuwan da doka ta ce idan sun faru ba za a ayyana dan takarar da ya samu nasara ba.

Zaben 2023: Sokoto

A cewar Farfesan, daga cikin abubuwan akwai tayar da fitina da zata kai ga tarwatsa zabe ko sace akwatin zabe, ko karbe na'urar zabe, ko a yi zabe ya wuce adadin yawan mutanen da ke a rumfa, duk suna sa a soke zabe, kuma akwai yanayin da idan ya faru doka bata yarda a ayyana sakamakon zaben ba har sai an sake gudanar da zaben cike gurbi sannan a hade sakamakon farko da na biyu a ayyana wanda ya lashe zaben.

Wannan lamarin ya sa wasu ‘yan Najeriya nuna damuwa akan abubuwan da suka yi sanadin ayyana zabukan a zaman wadanda basu kammala ba, yayin da wasu jama'a ke ganin ya kamata masu zabe su rinka yi wa kansu karatun ta natsu ta hanyar kauce wa duk abubuwan da ka iya kai ga ayyana zabe a matsayin wanda bai kammala ba. Wasu kuma na ganin kamata ya yi mahukunta su kara daukar matakan kauce wa faruwar hakan a gaba.

Saurari rahoton Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Ko Me Ke Sa A Ayyana Zabe A Matsayin Wanda Bai Kammala Ba?