Ko Aure Daga Wata Kabila Nada Fa'ida?

Auren wata kabila daban, kamar yadda yawancin matasa samari da ‘yan mata suka bayyana ra’ayoyinsu, ba bakon abu bane musamman ga al’uma da kuma kasa irin Najeriya.

Najeriya, kasa ce da masana suka bayyana a matsayin al’umar da ta kumshi daruruwan harsuna da al’adu daban daban, kuma suna cudanya da juna a wurare daban daban, kama daga wuraren ayyuka, makarantu, masana’antu da sauransu.

Ta dalilin haka ne dandalinvoa a shirinmu na samartaka ya sami zantawa da matasa daban-daban maza da mata domin ji ra’ayoyinsu akan yadda suke kallo da kuma yiwuwar kasacewar aure daga wata kabilar da ba tasu ba, ko hakan nada wani tasiri a zamantakewa da kuma kara fahimtar juna?

Yawancin matasa dai sun bayyana ra’ayoyinsu akan yiwuwar hakan musamman cikin yanayi na soyayya, domin kuwa a cewar wasu da dama, soyayya tsakanin matasa bata cika yin la’akari da banbacin kabila ba musamman haduwar makaranta, ko wurin aiki da makamantansu.

Domin Karin bayani, saurari cikakkiyar hirar a nan.

Your browser doesn’t support HTML5

Ko Aure Daga Wata Kabila Nada Fa'ida?