Al’uma na yi wa mata ma’iakata wani irin kallo da zarginsu da rashin kamun kai, mussamman ma idan aikin da macen ke yi ya danganci mu’amala da mutane da dama inji Zainab Rabiu Salisu.
Zainab Rabi’u ta bayyana haka ne yayin da suke zantawa da wakiliyar DandalinVOA, inda ta bayyana cewa sau tari, mata ma’aikata da ke zuwa wuraren aiki sun fi kamun kai fiye da wadanda basa zuwa ko suke zama gari banza .
Ta ce a matsayinta mace kuma yar jarida, aikinta na ba ta damar sanin mutune, a hannu guda kuma yana tattare da kalubale da dama, inda ta kara da cewa a mafi yawan lokuta idan ta je dauko labarai wani sa’ilin ita kadai ce mace a cikin duban maza.
Matashiyar ta kara da cewa wani lokacin kuwa akasin haka ake samu domin jama’a na marhaba da karbarta cikin natsuwa da kwanciyar hankali, a hannu guda kuwa a matsayinta mace wata rana abokan aiki maza kanyi wa mata kallon gazawa ko kasawa a harkar jarida.