Kisan Jamal Khashoggi Shiryayyen Abu Ne - Saudiyya

A halin da ake ciki kuma, shugabar hukumar binciken sirrin Amurka ta CIA Gina Haspel ta saurari sautin azabar da aka ganawa Jamal Khashoggi.

Kasar Saudiyya ta ce kisan wani dan jaridar kasar Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin kasar dake Istanbul hari ne da aka shirya bisa ga bayannan da Turkiyya ta bayar.

Wannan sanarwar, da kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya dauka, mai bincike na musamman na Saudiyya ne ya fidda ta.

Da da farko jami’an Saudiyya sun ce Khashoggi ya fita daga ofishin jakadancin da ransa kuma basu san inda ya nufa ba. Daga baya kuma suka ce ya mutu ne sanadiyar damben da yayi da wasu a ofishin. A bayanansu na baya-bayan nan kuma, hukumomin Saudiyar cewa suka yi Khashoggi ya mutu ne sanadiyar shake wuyansa da aka yi a lokacin da yayi kokarin ya bar ofishin don neman taimako.

Wasu rahottani sun ce shugabar hukumar leken asirin Amurka da ake kira CIA a takaice, Gina Haspel, wadda ta je Turkiyya don ta yi bincike akan mutuwar dan jaridar na Saudiyya Jamal Khashoggi, ta saurari sautin da aka dauka na azaba da kisan da aka yiwa dan jaridar.

Ana sa ran Haspel zata gana da shugaba Donald Trump a yau Alhamis don yi mishi bayani akan wannan batun.