Shugaban haramtacciyar kungiyar nan ta fafatukar kafa Biyafara, Nnamdi Kanu, ya sake bulla tare da shan alwashin dawowa Najeriya, inda a cewarsa, zai cigaba da fafatukar kafa kasar Biyafara. Ya zuwa yanzu dai an ji duriyar Kanu ne a kasar Isira’ila, inda ya yi jawabi tare kuma da aikawa da sako ga mabiyansa da ke Najeriya.
Idan an tuna dai tun bayan da sojojin Najeriya su ka kai wani samame a makwancin Kanu da ke kudu maso gabashin Najeriya, shugaban na IPOB ya bace sama ko kasa. Yanzu kuma kwatsa, sai aka ji ya sake bulla. To sai dai da alamar da kyar ya samu irin goyon bayan da ya samu a baya, gabanin farmakin da sojojin su ka kai saboda wasu ‘yan kabilar Ibo na waswasin tabbatuwar kasar ta Biyafara ko kuma, a kalla, nasarar gwagwarmayar.
Wata ‘yar kabilar ta Ibo mai suna Madam Williams, ta ce ita dai gani ta ke wargi kawai Kanu ke yi. Ta ce muddun Kanu ya dawo Najeriya to abubuwa za su kara rincabewa ne kawai. Shi kuwa wani dan kabilar Ibon mai suna Emmanuel Sabia ya ce ‘’Godiya ga Allah tun da ya na raye. Na ji cewa an gan shi a kasar Isira’ila ; sai dai ni fa ba na goyon bayan Biafara. ’’ Amma wani kuma mai suna Eze cewa ya yi ya aminta da lamirin kafa kasar Biafara, kuma muddun shugabansu ya dawo, gwagwarmayar kafa Biafarar za ta dawo.
Ga dai wakilinmu Lamido Abubakar da cikakken rahoto
Facebook Forum