Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Bauchi, sun gudanar da addu’oi na musamman a Jerusalem domin fatan a gudanar da zaben kasar ba tare da tashin hankali ba.
Shugaban hukumar aikin hajjin kiristocin jihar, Rev. Shua’ibu Byel, ya gayawa wakilin Murayar Amurka ta wayar talho cewa sun ziyarci manyan wuraren bautar ibada musamman inda shi kansa Yesu Almasihu ya yi ibadunsa a lokacin rayuwarsa.
Byel ya kuma yaba da yadda aka gudanar da zaben aksar ta Isra’ila wanda aka kamala a farkon makonnan ya na mai cewa an yi zaben cikinj tsabta ba tare da tashin hankali ba.
“Za ka ga mutane a tsanaki suna yada manufarsu ko a mota ko a kafa ko ta hanyar raba ‘yan takardun bayanai da kuma amfani da kafafen watsa labarai don cimma manufa a zabe su ko kuma ‘yan takarar suba tare da tada hankali ba.” In ji Byel.
Ya kuma yaba da yadda masu kada kuri’a su ke fita bisa lokacin da yake da shi a ranar ya je ya kada kuri’a ya kara gaba abinsa ba tare da wata matsala ba.
Daga karshe Malamin Kiristocin ya tabbatarwa jama’a cewa idan suka dawo zai nemi amincewar Musulmi don amsa gayyatar da zai yi don tattaunawa da kuma neman mafita cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna don yin zabukan da Najeriyar ke fuskanta.
Your browser doesn’t support HTML5