Hadakar Kiristocin Arewacin Najeriya ta CNNC, ta yi kira ga hukumomin kasar da su yi gaggawar ganin an saki Leah sharibu.
Sharibu ce kadai daliba Kirista cikin ‘yan matan Dapchi 110 da kungiyar Boko Haram ta sace a jihar Yobe a watan da ya gabata.
Kuma har yanzu ta na hannun kungiyar duk da cewa an saki sauran daliban.
Yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a yau Litinin a Kaduna, Kakakin kungiyar, Larry Yammai, ya nuna bacin ran kungiyar kan yadda har yanzu aka kasa sako Sharibu.
“Muna masu farin ciki da aka samu kubutar da ‘yan matan na Dapchi, amma muna bakin cikin ganin cewa an rike Leah Sharibu saboda addininta.” Inji Larry, kamar yadda jaridar Tribune ta wallafa a shafin yanar gizonta.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito kungiyar ta na kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya yi gaggawar shiga tsakani domin ganin an sako Leah.
A karshen makon da ya gabata, Sipeta Janar din 'yan sanda kasar, Ibrahim Idris, ya bayyana cewa ana gab da karbo Leah.
A baya ma shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen ganin an sako dalibar.
Matsayar Kungiyar Islama Ta MURIC Kan Rike Leah
A ranar Larabar da ta gabata, aka sako ‘yan matan Dapchin su 106 har da wani yaro guda, bayan da suka kwashe wata daya a hannun mayakan Boko Haram.
Daya daga cikin daliban da aka sako, ta bayyana cewa an ki sake Leah ne saboda addininta sannan ta ki amincewa ta saka hijabi.
Wannan labari ya janyo kakkausan suka daga sassa daban-daban na Najeriya.
Kungiyoyin addinin Islama sun yi ta Allah wadai da yunkurin da Boko Haram ta yi na mai da Leah Musulma.
Kungiyar Islama mai kare hakkokin Musulmai ta MURIC ta ce ba a tilasatawa mutum ya shiga addinin Islama.
Ta kuma yi kira ga hukumomi da su yi gaggawan ganin an sako Leah.
“Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta koma kan teburin tattaunawa domin ceto yarinya daya Kirista da ta rage a hannun kungiyar Boko Haram.” A cewar kungiyar ta MURIC kamar yadda jaridar Vanguard t wallafa a makon d aya gabata.
A ranar 19 ga watan Fabrairu aka daliban a makarantarsu da ke Dapchi a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.