PLATEAU, NIGERIA - Bikin wanda ake gudanarwa kowace shekara ana farawa ne ranar Jumma’a, wanda ake wa lakabin ‘Good Friday ko Jumma’a mai kyau, zuwa ranar Litinin.
Mabiya addinin Kirista na yin bikin ne don tunawa da mutuwa da tashin Isa Almasihu, wanda suka yi imani ya mutu ne don ceton bil’adama daga shiga jahannama, matukar sun yi imani da farillansa.
Rabaran Ishaku Sule daga Bauchi ya ce Easter lokaci ne da masu bin Yesu Almasihu zasu sadaukar da kai wajen yin rayuwa da ta dace da yin addu’o’i don kasa ta zauna lafiya.
Wata Malama Hauwa Danjuma Bello ta ce kamata yayi mabiya Kiristi su nuna kauna ga kowa su kuma tallafa wa mabukata.
Wasu dake gudun hijira a garin Vom dake Jihar Filato sun bayyana cewa zasu yi bikin na Easter ne cikin bakin ciki, saboda kisa da ‘yan bindiga suke yi masu.
Duk da yanayi na tashin hankali da matsin rayuwa da ake fuskanta, mabiya addinin Kiristan dai sun ce zasu dukufa ga yin addu’o’i don Allah ya daidaita lamura.
Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5