Yanzu haka dai garin damagaran ya dauki harama tun da aka gudanar da yakin neman zabe a hukumance, komai ya kankama inda jam’iyyu suka lika fastoci da kyallaye a tituna da jikin motocinsu.
WASHINGTON, DC —
‘yan siyasa na ta ganawa da magoya bayan su a birane da karkara, don kaucewa duk wani tashin hankali ko rigingimu ‘yan siyasa sun kira magoya bayansu da su gujewa haddasa fituna ko tsokana, kamar yadda Bazu Muhammed na jam’iyyar PNDS Tarayya yayi kiran.
Shima Abdul Majid na jam’iyyar Hakuri, cewa yayi magoya bayansu su bi doka, ya kuma ci gaba da cewa tunda suka fito daga kotu sun ci gaba da nuna halin ‘da’a da juriya da hakuri da biyayya.
Sha’aibu Musa babban mai shari’u a kotun Damagaran, ya ja hankalin ‘yan siyasa da magoya bayansu da su kiyaye doka da oda.
Saurari cikakken rahotan Tamar Abari.
Your browser doesn’t support HTML5