Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chadi: Bam ya tashi a garin Gitte


Shugaban Chadi Idriss Deby
Shugaban Chadi Idriss Deby

Garin Gitte nada kasuwa wadda take ci ranar Lahadi saboda haka sun kafa masu kula da tsaro suna bincikar kowa ya zo shiga kasuwar

Jiya Lahadi ranar kasuwar garin wani dan kunar bakin wake ya zo ya shiga kasuwar sai 'yan kato da gora da jami'an tsaro suka tareshi su bincikeshi.

Da aka hanashi shiga kasuwar sai ya tada bam dake jikinsa ya rasa ransa da jikata wasu talatin da suka hada da sojoji. Bayan wadanda suka mutu sojoji sun tada wuta saboda lamarin.

Dangane da harin da aka kai a wani kauye dake kusa da garin Gitte wasu 'yan mata guda biyu ne suka shiga kauyen inda suka tarar da mutane suna batun harin Gitte sai suma suka tada bam wanda ya kashe mutane shida tare da jikata wasu 17.

Ana kyautata zaton mutumin da ya tada bam a Gitte da 'yan matan tafiyarsu guda ce.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG