Kimanin Mutane Miliyan Dari Takwas Ke Fama Da Talauci A Duniya

Antonio Guterres

Ranar kawar da talauci ta duniya ta faro ne daga kasar Faransa a shekarar 1987, biyo bayan karrama mutanen da suka yi fama da tashe tashen hankula da tsananin yunwa

Yau ne ranar kawar da talauci na duniya, kamar yadda tarihin ya nuna ranar kawar da talauci ya farone a ranar 17, ga watan oktoban shekara 1987, abirnin Paris, a wannan rana dubban daruruwan mutane sukayi dandazo domin karrama mutanen da masifu iri iri dasuka hada da talauci,tashe tashen hankula da kuma yunwa ta shafe su.

Bayanai na nuni da cewa tun daga wannan ranace sai Majalisar Dinkin Duniya, ta hanyar kirkiro kudiri na arba’in da bakwai (47) mai lamba (196) ta amince da kasancewar ranar 17, ga watan Oktoban kowace shekara a matsayin ranar kawar da talauci ta duniya, da kuma gayyatar dukkan kasashe da su kebe ranar domin gabatarwa da kuma wayar da kan mutane cikin tsare tsaren gwamnatoci game da batun kawar da talauci.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Anthony Gutierrez, ya jinjinawa al’uma da kuma jaddada goyon baya da kimanin mutane miliyan dari takwas dake cikin kangin talauci a fadin duniya.

Yace akwai wasu da dama dake fuskantar matsanancin rashin aikin yi da na tsaro nuna bana rikice rikice da kuma canjin yanayi, hakkan na nufin a saurari ra’ayoyin mutane dake zaune cikin talauci sabili da haka hada hannu ya zama wajibi domin kawar da talauci ta hanyar mutunci.

Taken bikin ranar kawar da talauci na wannan shekarar shi ne "Amsa yekuwar ranar 17, ga watan Oktoba domin kawarda talauci," hanyar zaman lafiya domin tabbatar da al’uma dunkulalliya.

Your browser doesn’t support HTML5

Kimanin Mutane Miliyan Dari Takwas Ke Fama Da Talauci A Duniya - 3'26"