Ministan kiwon lafiya na Najeriya Dr. Isaac Adewale yace ranar 27 ga watan Satumbar wannan shekarar ne Cibiyar Dake Yaki Da Yaduwar Cututtuka ta samu labarin barkewar cutar kyandar biri a jihar Bayelsa.
Ministan yace a ranar 13 ga wannan watan ne aka tabbatar da kamuwar mutane bakwai da cutar a jihar. Cutar dai tana haddasa manyan kuraje.
Bullar cutar ya haifar da tsoro tsakanin ‘yan Najeriya musamman wuraren da ake cin naman biri,kamar wasu jihohin kudu-maso-kudu da kudu-maso-gabashin kasar.
Ministan yace sun sami sakamakon binciken da suka sa a yi musu kan samfura uku na cutar da suka tura zuwa Cibiyar Binciken Cututtuka ta Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya dake Dakar kasar Senegal.
Ko baicin jihar Bayelsa an samu bullar cutar a wasu jihohi takwas da suka hada da Akwa Ibom, Cross River, Ekiti, Rivers, Enugu, Lagos, Nasarawa da kuma Birnin tarayya, wato Abuja.
Shi ma babban daraktan Cibiyar Yaki Da Yaduwar Cututtuka ta Najeriya, Dr. Chikwe ya jadadda bukatar kawar da fargaba kan cutar. Yace tuni aka yiwa wadanda suka kamu da cutar magani kuma babu wanda ya rasa ransa sanadiyar cutar.
Ga rahoton Saleh Ashaka da karin bayani.
Facebook Forum