Keshi Ya Yi Fatali Da John Mikel Obi Da Emmauel Emenike

Coach Stephen Keshi speaks to members of the Super Eagles at practice in Abuja before their World Cup qualifier against Ethiopia.

Jagoran kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles, Stephen Keshi, yayi fatali da wasu ‘yan wasa irinsu John Mikel Obi da Emmanuel Emenike daga cikin ‘yan wasa 15 dake bugawa a kasashen waje da ya gayyata domin wakiltar Najeriya a gasar share fagen neman zuwa cin kofin kasashen Afirka da zata yi da kasar Chadi a ranar 8 ga watan Yuni.

Anyi waje rod da Mikel, wanda kungiyarsa ta Chelsea ta lashe kofin wasannin lig na Firimiya na Ingila, a saboda an ce babu jituwa tsakaninsa da Keshi, yayin da shi kuma Emenike dake bugawa kungiyar Fenerbache ta Turkiyya an ce da alamun tamaular ta fara barin jikinsa, domin wasansa ya kwanta sosai.

Wadanda aka gayyata dai sun hada da mai tsaron gida Vincent Enyeama, sai Ahmed Musa, OgenyiOnazi, Odion Ighalo, Aaron Samuel, da Kenneth Omeruo. Akwai kuma wasu sabbin ‘yan wasan da ba a taba gayyatarsu zuwa Super Eagles ba, ciki har da William Troost-Ekong dake buga tamaula a Netherl;ands, da Kingsley Madu na kungiyar AS Trencin ta kasar Slovakia da kuma Anderson Esiti dake wasa a kasar Portugal.

Najeriya zata buga wasannata da kasar Chadi a garin Kaduna a ranar 8 ga watan Yuni a wasannin share fagen neman wadanda zasu halarci gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2017.