Kungiyar wasan kwallon kwandon Amurka ta NBA za ta yi gasar wasanta na farko a nahiyar Afirka, sannan a filin wasanni na Ellis Park Arena da ke Johannesburg ta Afrika ta Kudu za a daga ranar 1 ga watan Agustar bana, inda Kulab din ‘Team Africa’ da ‘Team World’ zasu kara karkashin jagorancin dan wasan ‘Miami Heat’ Luol Deng dan asalin kasar Sudan da kuma Chris Poul na Los Angeles Clippers’.
Nahiyar Afirka ta haifar da fitattun ‘yan kwallon Kwando kamar su Hakeem Olajuwon daga Najeriya, sai Serge Ibaka daga Congo da kuma Dikembe Mutumbo daga Jumhuriyar dimukuradiyyar Congo. Duk da wadannan taurarin, wasan kwallon kwandon da jin jikin samun karbuwa a nahiyar. A shekarar 2010 ne da kungiyar NBA ta bude ofishinta na farko a Afrika ta Kudun don bunkasa wasan a nahiyar.
Deng ya bayyana farin cikinsa game da wannan wasa da za a yi a asalin nahiyar da ya fito. Shima kwamishinan na NBA Adam Silver yace yana cikin annashuwar yadda za ayi wasan karon farko a Afirka a kokarinsu na aiki tukuru da NBA ta ke yi don bunkasa wasan kwallon Kwando a Afirka.