Babbar kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuffuka tana zargin ‘yan kasar Kenya shida, ciki har da wasu manyan kusoshin gwamnati, kasancewa mutane da suka hura wutar fitina da ta biyo bayan zaben kasar a 2008.
Sunayen mutanen da kotun ta bayyana a yau laraba sun hada da minsitan ilmi William Ruto, ministan kudi Uhuru Kenyatta,da kuma ministan masana’ntu,Henry Kosgey. Saura sun hada da tsohon baturen ‘Yansanda Mohammed Husseini Ali, da shugaban wata tashar Radiyo,Joshua Arap Sang,da kuma sakataren majalaisar ministocin kasar Francis Kirimi Muthara.
Babban mai gabatar da kara gaban kotun Luis Moreno-Ocampo,yace zai nemi kotu ta bada sammacin akama mutanen.
A mataki na gaba,alkalan kotun zasu tsaida shawarar gabatar da tuhuma kan wadan nan mutane. Ocampo yace, mutanen sune kanwa uwargamin tarzomar da ta halaka kimanin mutane dubu daya da dari uku.