A cewar jami’in ba da agajin gaggawana NEMA da ke kula da yankin jahohin, Thikman Tanimu, gwamnatin jihar ta Kebbi ta yi watsi da mutanen jihar wadanda aka maido su daga jamhuriyar Nijar.
“Kafin a kawo su nan, an sanar da mu mun kuma sanar da jihohin nan cewa a yi tanadi mutanen suna zuwa, gwamnatin jahar Kebbi ba su zo sun dauki mutanen ba.” In ji Tanimu.
A cewar Tanimu akalla motoci 30 suka iso daga Nijar wadanda adadinsu ya haura 2000 kuma “mafi yawansu ‘yan jahar Kebbi ne, mutanen Sokoto ba su fi mutum 200 ba.”
Sai dai jami’in na NEMA ya ce daya daga jami’an hukumar ba da agaji gaggawa a matakin jaha mai suna Injiniya Chindo ya zo ranar alhamis din da ta gabata ya kuma gaya mai cewa ya baiwa gwamnati shawara kan yadda za a kwashi ‘yan gudun hijran.
“Daga baya da na kira shi, sai ya ce ai gwamna Sa’idu Dakin Gari ya ce ba mutanen jahar kebbi ba ne, kada a kawo mai mutanen da za su tada da hankali.” In ji Tanimu.
A lokacin da wakilin Muryar Amurka, Muratala Faruk Sanyinna, ya tuntubi jami’in hukumar ta NEMA na jahar ta Kebbi, wato Injinya Yahaya Chindo Jega, ya musanta zargin.
“Ba haka ba ne, ban ce mai ba ‘yan jahar Kebbi ba ne, yanzu haka munan nan tare da gwamna muna kokarin muga yadda za a kwaso su.” In ji Ijiniya Chindo.
A dai makon da ya gabata, hukumomin Nijar suka ce ‘yan gudun hijran Najeriya da ke yankin tsibirin Karamga da su fice daga yankin inda suka basu wa’adin mako guda, wa’adin da ya cika tun ranar litinin din da ta gabata.
Ga karin bayani a rahoton Murtala Faruk Sanyinna:
Your browser doesn’t support HTML5