Kebbi: Sarkin Kanya Ya Rasa Ransa A Hannun Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Shi

'Yan bindiga a yankin jihar Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da cewa barayin daji sun kashe Sarkin Kanya Alhaji Isa Daya, kwana biyu bayan sace shi tare da mutane tara.

Sai dai a cewar gwamanatin an kubutar da sauran mutane tara da aka yi garkuwa da su tare da basaraken.

Bayan da aka sace sarkin Kanya Alhaji Isa Daya da wasu mutane tara, gwamnatin jihar Kebbi ta ce ta dauki matakan ceto sarkin da sauran mutanen, to sai dai a iya cewa kaddara ta riga fata, domin sarkin shi kadai ne ba a ceto rayuwarsa ba.

Mai baiwa gwamnan jihar Kebbi shawara na musamman akan harkokin sadarwa da tsare-tsare, Abdullahi Zuru ya ce Sarkin ya hadu da ajalinsa a kokarin kubutar da su daga hannun barayin.

Ita kan ta masautar Kanya ta bakin Makaman Kanya Muhammadu Namakuku, ta tabbatar da rasuwar basaraken.

Yanzu haka dai jama'a na kan nuna alhini a kan wannan rashin na sarkin Kanya Alhaji Isa Daya, kamar yadda Farfesa Tukur Muhammad Baba ya nuna alhininsa tare da yin kira ga mahukuntan Najeriya.

Kasancear sarakuna sune tamkar iyayen al'umma, yanzu alamu na nuna yadda ayukan 'ya bindiga suka karkata garesu, kamar yadda ake gani lokuta daban daban.

'Yan bindiga sun kai hari ga Sarkin Fulanin Bungudu Allah ya tserar da shi, kuma sun tare Sarkin Birnin Gwari shima ya samu tsira, da Sarkin Gobir Na Sabon birni da suka kashe, kuma ga shi yanzu sun kai samame gidan Sarkin Rafin Gora ba su same shi a gida ba, sai kuma sarkin Kanya da suka dauka suka kasha.

Yanzu dai Sarkin Kanya Alhaji Isa Daya ya bar duniya, kamar yadda ya faru ga Sarkin Gobir cikin watan Agustan wannan shekara.

Domin Karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.

Your browser doesn’t support HTML5

Sarkin Kanya Ya Rasa Ransa A Hannun Wadanda Su Ka Yi Garkuwa Da Shi - 3'55"