A farkon wannan mako ma an samu hasarar rayuka akasari na ‘yan sa kai a jihar kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya da kawo yanzu ba'a san adadin su ba.
‘Yan Najeriya musamman na arewacin kasar na ci gaba da fuskantar tashin hankali sanadiyar kissan gilla da ‘yan bindiga ke yiwa jama'a duk da ko kokarin da mahukunta ke yi na shawo kan matsalolin na rashin tsaro.
A jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya jama'a na ci gaba da jimami akan kisan gilla da ‘yan bindiga suka yi wa jami'an tsaro na sa kai wanda ke taimakawa wajen samar da tsaro a yankunan su.
Lamarin ya faru ne sanadiyar arangama da suka yi da ‘yan bindiga wadanda ake sa ran sun gudano ne daga jihar Neja inda ake fatattakar su, inda suka yiwa ‘yan sa-kai da suka yi shirin tarbon su a jihar Kebbi kwanton bauna.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bakin kakakinta a jihar Kebbi SP na ‘yan sandan Nafi'u Abubakar ta tabbatar da an yi arangama tsakanin barayin da ‘yan sa kai.
Jama'ar yankin dai na ganin ya kamata a rika samun kawance tsakanin jami'an tsaro na hukuma da na sa kai domin kaucewa samun irin wannan matsalar nan gaba, da yake ‘yan sa kai na bayar da gagarumar gudunmuwa wajen kare yankunan su.
Ita kuwa rundunar 'yan Sandan tace dama suna aiki tare kawai tsotsai ne ya rutsa da su a wannan karon.
Jama'ar yankin kudancin jihar Kebbi na daga cikin jama'ar yankunan arewa da matsalar rashin tsaro ke hanawa bacci da idanu biyu rufe, kuma sun jima suna kokawa akan matsalolin wadanda ko sun yi sauki sai su sake juyowa kuma mahukumta na ta cewa suna kokarin shawo matsalolin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5