Kazamin Fada Ya Barke A Kudancin Afghanistan

Wani kazamin fada ya barke a kuduncin Afgahnistan, bayan da mayakan Taliban suka kai wani hari a wata Gunduma.

An dai samu bayanai masu karo da juna kan wannan arangama, daga jami’an kasar ta Afgahnistan da mayakan na Taliban, kan wannan fada da ya barke a yau Litinin a Gundumar Sangin dake Helmand, wanda ita ce mafi girma cikin Larduna 34 dake Afgahnistan.

Kakakin gwamnati, Omar Zwak ya fadawa Muryar Amurka cewa masu ta da kayara baya sun kai hare-hare a shingayen binciken jami’an tsaro, amma kuma an dakarun gwamnatin sun fatattake su.

Ya kuma ce an kashe maharani da dama kana an raunata wasu, amma kuma ba fadi ko an akshe wasu daga cikin dakarun kasar ba.

A daya bangaren kuma wani Kakakin Taliban ya ikrarin cewa sun kawar shingayen binciken jami’an tsaro har 25 da kuma wasu sansanoni a Sangin, kuma an ci gab ada fafatawa.

Ya kara da cewa wani dan kunar bakin wake ya kai hari a farfajiyar wani sasanin sojin kasar inda ya kashe tare da raunata sama da jami’an gwamnatin 100.

Kungiyar ta Taliban dai kamar yadda rahotanni ke nunawa ta kan kara adadin mutanen da ta jikkata a duk lokacin da ta kai hari.