Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wutar Daji Ta Yi Barna A Kasar Chile


'Yan Kwana-kwana na kokarin kashe gobarar daji.
'Yan Kwana-kwana na kokarin kashe gobarar daji.

Wutar dajin da ta lakume sama da rabin kadada miliyan daya a kasar Chile ta ja da baya, bayan da jiragen saman Amurka da Rasha masu dauke da manyan tankuna hade da kwararru a fannin kashe wutar daji suka je yankin.

An samu akalla wutar daji 118 inda 59 daga cikinsu suke ci babu kakkautawa a cewar wani jami’in kula da dazukan kasar ta Chile.

Hukumomin sun ce rashin zama cikin shirin ko-ta-kwana da kuma tsarin noma na bai-daya da ake yi a kasar, sun taimaka wajen haddasa wannan wutar daji mafi muni a cikin ‘yan shekarun nan.

A yankin Portezuelo dake da tazarar kilomita 400 daga babban birnin kasar na Santiago, al’uomomin yankin sun yi kokarin hada wutar-katanga da za ta hana gobarar dajin kaiwa ga yankunansu, amma hakan ya cutura bayan da igiyar iska ta sauya inda take tafiya.

Wannan hadarin na wutar daji ya sa ‘yan sanda da sojoji sun kwashe mutane da dama daga yankunansu a aksar ta Chile.

XS
SM
MD
LG